1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murabus ɗin Köhler koma-baya ne ga Afirka

June 4, 2010

Horst Köhler dai mai muradin ganin an nuna wa Afirka adalci ne a al'amuran ƙasa da ƙasa

https://p.dw.com/p/NiXW
Tsohon shugaban Jamus Horst Köhler lokacin da yake jawabin yin murabusHoto: AP

Bari mu fara daga nan Jamus inda a farkon mako ba zato ba tsammani shugaban ƙasar Horst Köhler mai matuƙar ƙaunar nahiyar Afirka yayi murabus. A rahotonta jaridar Tageszeitung cewa ta yi Horst Köhler ba zai je birnin Wagadugu ba, 'yan ƙasar Burkina Faso na cikin juyayi domin shugaban na Jamus ba zai kai ziyarar aikin da ya shirya kaiwa ƙasar ta Yammacin Afirka a wannan Lahadin ba. Jaridar ta bayyana wannan murabus da cewa wani babban koma-baya ne ga ƙasashen Afirka kasancewar tsohon shugaban na Jamus, tun bayan hawansa kan wannan muƙami ya duƙufa wajen ganin wannan nahiya ta samu taimakon da take buƙata domin fita daga ƙangin wahalhalu da take fama da su.

Afrika Frankreich Gipfel Nicolas Sarkozy
Shugaban Faransa Nikolas Sarkozy a lokacin taron Faransa da ƙasashen AfirkaHoto: AP

To sai dai yayin da a hannu ɗaya ake fargabar koma-bayan da Afirka za ta samu sakamakon wannan murabus na Köhler, a waje ɗaya kuma rahotanni masu ƙarfafa guiwa aka samu biyo bayan taron ƙolin da ya gudana tsakanin shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da takwarorinsa na Afirka. A rahotonta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito Sarkozy na cewa Faransa za ta haɗa kai da dukkan ƙasashen nahiyar Afirka amma ba waɗanda Faransa ta yiwa mulkin mallaka kaɗai ba. Jaridar ta ci-gaba da cewa Sarkozy zai mayar da kansa tamkar wani lauyan Afirka bayan ya jaddada goyon bayansa ga bawa Afirka babban matsayi a gamaiyar ƙasashen duniya. Ba daidai ba ne Afirka ta kasance sahun baya wajen ɗaukar muhimman matakai ga ƙasashen duniya domin ba za a iya warware ko da ɗaya daga cikin manyan matsalolin duniya ba tare da shigar da nahiyar Afirka ba.

Sannu a hankali kamfanonin Afirka na farfaɗowa, inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai nuni da wani nazari da ƙungiyar Boston Consulting Group ta ƙasar Amirka ta gudanar inda ta gano cewa a tsukin shekaru 10 da suka wuce ƙarfin tattalin arzikin Afirka ya ƙaru ƙwarai da gaske sannan kamfanonin nahiyar suna taka rawar gani a fagen kasuwancin ƙasa da ƙasa. To sai dai kuma jaridar ta ce bai kamata sakamakon wannan nazarin ya kawad da gaskiyar cewa kason Afirka a harkokin kasuwancin duniya bai haura kashi biyu cikin 100 ba yayin da shekaru 50 bayan lokacin da ɗaukacin ƙasashen Afirka suka samu mulkin kai wannan kason ya kai kashi 10 cikin 100. Hakazalika duk da dubban miliyoyin kuɗaɗen taimakon raya ƙasa, Afirka Ta Kudu ce kaɗai za ta iya tinƙaho da wani ci-gaban masana'antu, yayin da shugabannin Afirka da muƙarrabansu kaɗai suke cin gajiyar ɗinbim albarkatun ƙarƙashin ƙasa na wannan nahiya.

Südafrika Nationalmannschaft FiFA 2010 Weltmeisterschaft Südafrika
'Yan wasan ƙwallon ƙafar Afirka Ta kuduHoto: AP

Yayin da ya rage kwanaki kaɗan a fara gasar cin kofin ƙwallon ƙafar duniya a Afirka Ta Kudu labarin gano wasu sansanonin 'yan ta'adda a maƙwabciyar ƙasar wato Mozambik ya ta da hankula. Jaridar Neues Deutschland ta rawaito cewa 'yan tarzoma na shirin kai hari akan 'yan wasan ƙwallon kafa da masu kallon wasa. Murnar karɓar baƙoncin gasar ta kusan komawa ciki sakamakon harbe harben da ya wakana a ƙarshen makon jiya tsakanin wasu ƙungiyoyi dake gaba da juna lokacin wasan ƙwallon ƙafa na yara a birnin Cape Town inda mutum biyu suka rasu. Fata dai a nan shi ne a yi gasar ƙwallon ƙafar duniyar lafiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu