1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye ta bulla a Britania

Zainab A MohammadApril 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bu71

A Scotland din Britania an samu bullar kwayar cutar murar tsuntsaye da ake kira H5N1 a jikin wani tsuntsu da aka tsinta mace yau.Britania ta kasance kasata 14 a nahiyar turai da wannan cuta data kashe mutane 109,tun bullar ta 2003.Jamian zartarwa na Scotland din dai sun tabbatar dacewa wannan mataccen tsuntsu da aka samu gabashin yankin a makon daya gabata na dauke da kwayoyin wannan cuta.To sai dai ya zuwa yanzu hukumomi a Britania na kokarin kwantar da hankalin mutane ,adangane da tsoron yiwuwar yaduwar wannan cuta zuwa biladama.Charles Milne dai babban likitan dabbobi ne a Scotland.Ya zuwa yanzu dai an umurci dukkan masu gonakin tsuntsaye dake Edinburgh dasu rufesu acikin wuraren kiwo.A wannan yanki kadai dai akwai gonakin tsuntsaye kimanin 175,wadanda ke dauke da tsuntsaye million 3.1,daga cikinsu kuwa dubu 260 na yawansu ne ba tare da killacewa ba.