1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye ta bulla a Italiya, Girika da kuma Bulgariya

February 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8W

Masassarar tsuntsaye ta bulla a kasashen Italiya, Girika da kuma Bulgariya, karon farko da aka tabbatar da bullar ta a kasashen kungiyar tarayyar Turai EU. Kamfanin dillancin labarun Italiya ANSA ya ce an tabbatar da cewa nau´in kwayoyin H5N1 na murar tsuntsaye yayi sanadiyar mutuwar wasu agwaji 17 a kudancin Italiya da kuma tsibirin Sicily. Shi ma ministan aikin gona na Girika ya tabbatar da cewar wani gwaji da aka gudanar a dakin binciken kimiya ya nuna cewa kwayoyin H5N1 suka halaka agwaji 3 a arewacin kasar. Sannan gwaje-gwajen da aka yi a Birtaniya sun tabbatar da kwayoyin cutar mai kisa a jikin wasu agwajin daji da aka gano a kusa da kan iyakar Bulgariya da Romaniya. A cikin wannan makon dai ne murar tsunstaye ta bulla a tarayyar Nijeriya.