1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye ta halaka mata biyu a Indonesia

February 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8P

A kasar Indonesia mutane biyu sun rasu sakamakon kamuwa da nau´in murar tsuntsayen ne mai kisa wato H5N1. Kamar yadda ma´aikatan kiwo lafiya a wani asibiti dake birnin Jakarta suka nunar, an gano kwayoyin H5N1 a jikin wasu mata biyu wadanda suka rasu a cikin makon jiya. An tabbatar da haka ne bayan gwajin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi. Yanzu haka dai yawan wadanda matsananciyar murar tsuntsaye ta yi ajalinsu a Indonesia ya kai mutum 18. A karon farko a jiya asabar aka ba da sanarwar bullar nau´in na H5N1 a wasu kasashen KTT da suka hada da Italiya, Girika da kuma Bulgariya.