1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye ya kashe mutum guda a Nigeria

February 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuSf

Hukumar kula da lafiya ta MDD ta bayyana cewa an dauki samfurin farko na cutar data kashe wata mace a tarayyar Nigeria da ake zargin cewa murar tsuntsaye ne,daya hallaka mutumin farko da bullarsa a nahiyar Afrika,domin gwaji a Britania.Hukumomin tarayyar ta Nigeria sun sanar dacewa ,gwajin da sukayi marigayoyar mai shekaru 22 da haihuwa a birnin Lagos jiya,na nuni dacewa kwayar cutar murar tsuntsayen mai nauin H5N1 ne ya kashe ta,sakamakon fige kasar dake dauke da wannan cuta datayi.Kakakin hukumar kula da lafiya ta mdd Gregory Hartl yace ,zaayi gwajin samfurin a cibiyar binciken hukumar dake arewacin London.Nigeria dake da mafi yawan alumma a nahiyar Afrika,itace kasa ta farko da wannan cuta ta murar tsuntsaye ta bulla a gonakin kiwon kaji da dangoginta.Da bullar cutar dai ta yadu zuwa jihohi 17 daga cikin 36 a shekarar data gabata,duk da matakan killacesu da haramta kasuwancinsu daga ketare da akayi.