1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musayar wuta tsakanin Isra'ila da Libanon

August 4, 2010

A jiya Talata an samu musayar wuta tsakanin sojin Israila da na Libanon da aka a girkr kan iyakokin kasashen biyu .Akalla mutane uku suka rasa rayukansu a baya ga wasu da dama da suka samu rauni

https://p.dw.com/p/Oc6J
Musayar wuta tsakanin Isra'ila da LibanonHoto: AP

Wannan aramgamar dai na zaman irinta na farko da aka fuskanta tsakanin dakarun biyu bayan wasu shekaru da suka gabata da ta yi sanadiyar mutuwar sojoji guda uku da kuma wani ɗan jarida ɗaya. An samu wasu sojojin Isra'ila da dama da su kuma suka samu raunuka. Ko da yake an samu lafawar wannan rikici har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar. Abin da ka iya rura wutar wannan rikici shi ne kalaman Ghazi Ardi minista kuma jami'in gwamnatin Libanon wanda ke cewa:

"Ɗokacin 'yan ƙasar Libanon za su kare ƙasarsau da mutuncinsu. Ba za mu iya ci gaba da fuskantar barazana daga Isra'ila ke yi ga rayuarmu ba. Wajibi ne gamayar ƙasashen duniya ta daina kawaici da take yi game da matakan ta'addanci da Isra'ila ke ɗauka. In har Isra'ila da masu goyon bayanta na bukatar shiga babban yaƙi to mu kuma muna da yancin kare ƙasarsmu. Sam wannan yaƙi ba zai zama tamkar wani buki na anashwa ga Isra'ila ba. Ta taɓa shan kayi zata kuma sake shan kayi ba tare da la'akari da makaman da take amfani da su ba".

Ƙasar Isra'ila ta ɗora laifin ta da wannan hargitsi akan Libanon. Ta ce za ta shigar da ƙara a gaban Majalisar Ɗinkin Duniya. An dai fuskanci ɓarin wutar ne a lokacin da da 'yan ƙasar ta Iara'ila suka so sare wani itace dake wannan yanki na iyakar ƙasashen biyu. Ɓangarorin biyu sun yi gardama akan mallakar ɓangaren da itacen yake. An dai samu hoton wani bayahude dake ƙoƙarin kutsawa wannan yaki da injin sare itatuwa. Daga nan kuma 'yan ƙasar ta Libanon suka yi harbi cikin iska a matsayin gargaɗi. Yahudawan kuma suka ce sun mai da martani ne bayan da aka yi masu harbi.

A dai yankin dake kudancin Libanon an girke dakarun kawantar da tarzoma dubu 13 da ba su yi wani kataɓus domin kwantar da wannan rikicin ba. Timur Goskel da ya taɓa aiki da dakarun ya ce da kamata yayi dakarun su iya tinkarar duk wata matsala irin wannan da ka iya tasowa a wannan yanki:

"Muddin babu wani ɓangare na uku da yai katsalandan a wannan rikici, muddin wannan alamari na tsakanin sojojin Libanon da na Isra'ila muddin ba a bukatar rura wutar rikicin ana bukatar samun taimakon Majalisar Ɗinkin Duniya domin kwantar da shi. Abin da ke da muhimmaci kada a samu wata ƙasa ta uku da za ta shiga wannan rikici. Idan har mutun na aiki tsakanin rundunar soja guda biyu dole ne ya kwance masu damara ko da ma a ce abin zai shafi shi kansa ne."

Timur Goskel dai yayi wannan magana yana mai nuni da kungiyar Hizbullah dake da angizo a kudancin Libanon. A ma shekarar 2006 sai da Hizbullah ta shafe makonnin huɗu tana gwabaza yaKi da Isra'ila. Ko da yake babu wani mataki na shiga faɗa da Hizbullah ta ɗauka tun daga wannan lokaci amma har yanzu tsugune ba ta ƙare a wannan yanki ba. Shugaban Siriya Bashar Al-Assad yayi fira da takwaransa na Libanon ta waya inda yace suna a ɓangaren Libanon.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal