1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musharraf ya tsallake rijiya da baya a wani haɗarin alikofta

October 8, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8z
Daya daga cikin jiragen sama masu saukar ungulu 3 dake yiwa shugaban Pakistan Pervez Musharraf rakiya, yayi hadari a bangaren kasar na yankin Kashmir, inda ya halaka mutane 4 dake cikin sa. Sai dai shugaban bai samu rauni a wannan hadari wanda jami´an soji suka danganta shi da lalacewar inji ba. Musharraf ya je yankin na Kashmir ne don halartar bukin cika shekaru biyu da aukuwar mummunar girgizar kasar nan ta ranar 8 ga watan oktoban shekara ta 2005, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 80. A karshen mako dai ´yan tawaye 50 da sojoji gwamnatin Pakistan 20 aka kashe a wani kazamin fada da aka gwabza a wani yanki na magoya bayan Taliban dake kan iyaka da Afghanistan.