1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi a duniya na bikin sallah babba

Gazali Abdou TasawaSeptember 12, 2016

Al'ummar Musulmi a kasahen duniya daban-daban na gudanar da bukukuwan babbar salla wacce take daya daga cikin bukukuwan sallar da addinin Muslunci ya wajabta ga Musulmi.

https://p.dw.com/p/1K0Iu
Bukukukuwan babbar sallah a duniya
Bukukukuwan babbar sallah a duniyaHoto: Reuters

A yayin da aka gudanar da hawan arfa a ranar Lahadi 11 ga wannan wata na Satumba da muke ciki, a Litinin 12 ga wata ana gudanar da bukukuwan babbar sallah, inda kuma Alhazai zaa su gudanar da jifan shaidan a kasar Saudiyya, aikin da ke zaman cikamakwan ayyyukan da aka wajabta yayin aikin hajji. Al'umma da dama dai na gudanar da jifan shaidan din cike da tsoro da fargaba, kasancewar sa wanda ke cike da hadari saboda cunkoson al'umma yayin gudanar wa.

A aikin hajjin shekarar da ta gabata ta 2015 dai, alhazzai 2,300 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wani turmutsitsi da ya wakana a lokacin aikin na jifan shaidan a ranar 24 ga watan Satumba. A kasashen Musulmi da dama inda za a gudanar da bukukuwan sallar layyar za a share tsawon yini ana yanka dabbobi musamman raguna da kuma ziyartar dangi dama aminnan arziki.