1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi na ci-gaba da nuna fushinsu ga paparoma Benedict na 16

September 16, 2006
https://p.dw.com/p/BujP

Musulmi a duniya baki daya na ci-gaba da nuna fushinsu game da kalaman da paparoma Benedict na 16 yayi dangane da addinin Musulunci. A birnin Kairo da Zirin Gaza da wasu sassa na kasar Indiya an gudanar da zanga-zangar yin tir da wannan furucin. Ita ma kungiyar kasashen musulmi ta duniya wato OIC mai membobi kasashe 57 ta zargin Paparoma da nuna batanci ga addinin Islama. A kuma halin da ake cikin fadar Vatikan na kokarin rage irin sabanin da hakan zai janyo. A cikin wata sanarwa da ya bayar kakakin Vatikan Federico Lombardi ya ce ko kadan Paparoman ba ya nufin cin mutuncin musulmi. A wata lacca da yayi a lokacin ziyarar kwanaki 6 da ya kawowa Jamus paparoma Benedict ya rawaito wani sarkin sarakunan Kirsta a karni na 14 wanda ya ce Annabi Mohammad (SAW) ya kawo miyagun abubuwa, domin ya ba da umarni da a yada addinin Islama da bakin takobi. Kalaman na sa ya kuma ta da hankalin musulmi a kasar Turkiya, inda zai kai ziyara a cikin watan nuwamba.