1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmin Jamus na kare kansu daga tuhumar gama gari ta ta'addanci da ake yi musu.

YAHAYA AHMEDAugust 25, 2006

Musulimin Jamus sun fito fili suna bayyana rashin amincewarsu da wata tuhumar gama gari da ake yi musu, na kasancewa 'yan ta'adda, sakamakon yunƙurin nan da wasu 'yan ƙasar Lebanon suka yi na ta da bamabamai cikin jiragen ƙasa a ƙarshen watan da ya gabata.

https://p.dw.com/p/BtyW
Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Wolfgang Schäuble
Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Wolfgang SchäubleHoto: AP

Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Jamus, Wolfgang Schäuble, na iya kasancewa ɗaya daga cikin wadanda suka janyo wannan sabuwar muhawarar, saboda shi ne ya yi kira ga musulmin ƙasar nan, a matsayinsa na jagoran hukumar kula da harkokin tsaron cikin gida, da su bayyana a fili cewa suna tir da ayyukan ta’addanci. Idan ko ba su yi haka ba, za a iya yi musu saniyar ware a ɓangaren jama’a. To ko yaya su musulmin ke ganin wannan kiran? Aiman Mayzek, babban sakataren Majalisar Ƙoli ta Musulmin Jamus, ya ce babu wani dalilin yin wannan kiran da minista Schäuble ya yi. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Tun harin da aka kai a Madrid da London ne muka bayyana dalla-dalla cewa, aikata miyagun laifuffuka da ta’addanci ba sa cikin addinin islama. Duk wasu laifuffukan da aka aikata, to da sunansu ne ya kamata a yi matashiya da su, amma ba da sunan addinin Islama ba. To a yau ma muna nanata hakan.“

Kenan Kolat, shugaban gamayyar Turkawa ta birnin Berlin, shi ma ya bayyana cewa, ba a ko yaushe za a yi ta bukatar musulmi su fito su ce suna watsi da ta’addanci ba. Ai Jamusawa ma ba a bukatarsu su yi haka, idan ’yan ƙasarsu suka gudanad da wani ɗanyen aiki. Bayan yunƙurin da aka yi na ta da bamabamai a cikin jiragen ƙasa a nan Jamus, musulmi da dama na ganin cewa an ata ƙara tuhumarsu. Wani ɗan ƙasar Lebanon, ƙasar da waɗanda ake tuhumar suka fito, ya faɗa wa gidan talabijin ɗin ARD na nan Jamus cewa:-

„Kusan duk jaridu na cike ne da rahotanni kan ’yan kasar Lebanon. Wannan kuwa ai ba abin da ya dace ba ne.“

A halin da ake ciki yanzu dai, kamar ana kusan duk wata sadaswa tsakanin Jamusawa da musulmi ne ta hanyar kafofin yaɗa labarai. Ba sa cuɗanya da juna, inji mai unguwar Neukölln da ke birnin Berlin, Heinz Buschkowsky. A unguwar Neukölln ɗin ne kuwa aka fi yawan al’umman Lebanon da ke zaune a nan Jamus. Amma a nan ma, ana lura da wani babban giɓi na rashin cuɗanya da juna tsakanin Jamusawan da baƙi, inji mai unguwa Buschkowsky. Ya ƙara da cewa:-

„Ɗaya daga cikin dalilan da ke janyo haka kuwa shi ne, mafi yawan baƙin suna tafiyad da halin rayuwarsu ne a keɓe daga sauran jama’a. Ko a gidajen shan ti ne, ko a masallatai a ran juma’a ne, sauran jama’a ba sa sanin abin da ake tattaunawa a nan.“

Jami’an tsaro a nan Jamus dai sun ƙiyasci cewa akwai mutane kimanin dubu 2 zuwa dubu 3, musulmi, waɗanda a shirye suke su shiga cikin duk wasu tashe-tashen hankulla. A ganin hukumomin tsaron dai, duk da cewa yawansu wato bai taka kara ya karya ba, idan aka yi la’akari da jumlar musulmin da ke nan Jamus, wadda ta kai miliyan uku da dubu ɗari 3, amma hakan ma na iya janyo hauhawar tsamari a yanayin zamantakewa a nan ƙasar. To a ɓangaren hukumomin ke nan. A ɓangaren Majalisar Ƙolin ta Jamus kuma, bisa cewar Aiman Mayzek, al’umman ƙasar ne ke janye kansu daga sauran musulmin:-

„Muna ƙarancin samun bayanai daga ’yan ƙasar, wadanda za su iya fitowa fili su amince da mu su faɗa mana cewa: ku musulmi ma ’yan wannan ƙasar ne. Muna da tushe ɗaya. A daura da haka, babu abin da muke ta ji sai kiraye-kiraye na sanya takunkumai da tsananta matakan tsaro.“

A cikin watan Satumba mai zuwa ne dai ministan harkokin tsaro Wolfgang Schäuble, zai gana da wakilan ƙungiyoyin musulmi na nan Jamus. Ya ce yana son ya tabbatar musu cewa, addinin Islama, wani ɓangare ne na halin zamantakewa da aka amince da shi a nan Jamus da ma Turai gaba ɗaya. Ministan ya ƙarfafa cewa, ana gayyatar duk wata ƙungiyar islama zuwa wannan taron, idan ta amince da kundin tsarin mulkin Jamus tamkar tushen tafiyad da harkokin mulki a nan ƙasar, amma ba shari’ar musulunci ba. Taron dai zai tattauna batun hulɗa ne tsakanin musulmin da ƙasar Jamus da kuma tsarin koyad da addinin musulunci a makarantun hukuma. Amma mafi yawan musulmin na bayyana fargabar cewa, idan an zo gun taron, babub abin da zai fi mamaye ajandar, illa batutuwan harkokin tsaro.