1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 10 sun rasa rayukansu a tashin wani bam a Iraqi.

July 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bupv

A ƙalla mutane 10 ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu yayin da wani bam da aka dasa cikin mota ya tashi a arewacin Iraqi. Wani rahoton da ’yan sandan ƙasar suka bayar ya ce mutane 7 kuma sun ji rauni, a harin wanda ya auku a ƙauyen Beiji, mai nisan kilomita ɗari 2 da 40 a arewacin Bagadaza.