1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 15 sun mutu a Kamaru

Ramatu Garba Baba
July 14, 2017

Bayanai daga Kamaru na cewa mutane 15 ne suka yayin wasu sama da 40 suka jikkata sakamakon harin Bam a yankin Waza na kasar.

https://p.dw.com/p/2gZxC
Kamerun Kolofata Selbstmordanschlag Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

A kasar Kamaru, mutane akalla goma sha biyar ne aka tabbatar sun mutu yayin da wasu 45 kuwa suka sami rauni sakamakon harin bam da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai yankin Waza na kasar. Rahotanni sun ce maharan su biyu sun tayar da bama-baman da suka yi jigida da su ne a yankin wanda ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamarun. Ma'aikatar tsaron kasar ta danganta harin da irin wadanda kungiyar Boko Haram ta saba kai wa.

An dai kai harin ne a ranar Larabar da ta gabata da misalin karfe tara da rabi na maraice agogon kasar yayin da jama'a ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta tabbatar.