1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 30 sun mutu a hare-haren Madagali

Mouhamadou Awal Balarabe
December 9, 2016

Wasu mata biyu sun tada bama-baman da ke daure a jikinsu a kasuwar Madagali da ke jihar Adamawar Najeriya, inda mutane da dama suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jikata.

https://p.dw.com/p/2U2Qd
Karte Nigeria mit Madagali im Bundesstaat Adamawa

Akalla mutane 30 sun rasa rayukansu yayin da dama suka jikata a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da suka wakana a kasuwar garin Madagali da ke jihar Adamawa a tarayyar Najeriya. Kakakin rundunar sojojin Najeriya Badare Akintoye wanda ya tabbatar da wannan labarin, ya ce wasu mata biyu ne suka tayar da bama-bamai da ke daure a jikinsu a lokacin da ake tsaka da harkar saye da sayarwa.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan hare-hare ya zuwa yanzu. Amma suna kama da wadanda Kungiyar Boko Haram ta saba kaiwa a Najeriya tun shekaru bakwai da suka wuce. Sai dai harin ya zo ne kwanaki biyu bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a taron koli da ke gudana a Dakar na Senegal cewar an kusa kawo karshen 'yan Boko Haram a Najeriya.

Fiye da mutane dubu 20 ne suka rasa rayukansu yayin da miliyan biyu da dubu 500 suka kaurace wa matsugunsu tun bayan da kungiyar Boko Haram ta fara kai hare-hare a yankin Arewa maso gabashin Najeriya a shekara ta 2009.