1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 53 suka mutu dakamakon ambaliya a Afganisaan

November 18, 2006
https://p.dw.com/p/BubP

Mutane kimanin 53 suka rasa rayukansu a ambaliyan ruwa daya ritsa da yankunan tsaunuka dake yammacin kasar Afganistan,akasarinsu yara kanana,ayayinda wasu mutanen suka bace.Babban jamiin rundunar yan sanda dake gunduwar Badghis Muhammad Ayub Niazi,ya sanar dacewa ambayan ruwan ya kashe mutane 47 a yankin Balamurghad,kana wasu yara guda 6 a yankin Ghormach dake makwabtaka.Jamiin kiwon lafiya Abdullahi Fahim yace akwai mutane da dama da suka bace,sakamakon wannan abaliyan wadanda kuma baa san makomarsu ba.Yau ne dai jamian ceto suka isa yaukunan tsaunukan da jakuna dauke da kayyakin tallafi.