1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 7 sun rasa rayukansu a wata sabuwar faɗa da ta ɓarke a Sri Lanka.

November 23, 2006
https://p.dw.com/p/Buai

A wata sabuwar fafatawar da ta ɓarke tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan ƙungiyar nan ta Tamil Tigers a ƙasar Sri Lanka, rahotanni sun ce jami’an tsaro 7 ne suka rasa rayukansu, sa’annan a ƙalla 10 kuma suka ji rauni. Babu dai bayanai kan asarar da ’yan tawayen suka yi. Amma wani kakakinsu ya faɗa wa maneman labarai cewa, wani rukunin dakarun gwamnatin tare da tankunan yaƙi da dakarun igwa da kuma jiragen sama ne suka kai musu hari a gabashin ƙasar, abin da ya janyo ɓarkewar ɗauki ba daɗin. A nata ɓangaren, gwamnatin Sri Lankan ta yi inkarin zargin ’yan tawayen na Tamil Tigers, inda ta ce ’yan tawayen ne suka saɓa wa ƙa’idojin yarjejeniyar tsagaita wuta.

A wannan shekarar kawai, yawan sojojin gwamnati da mayaƙan ’yan tawayen da kuma fararen hular da suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulla a Sri Lankan, ya fi dubu 3.