1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 84 suka halaka a harin ta'addancin Faransa

Yusuf BalaJuly 15, 2016

Shugaba Francois Hollande ya bayyana cewa babu wani dalili na kebe wannan hari daga cikin harin ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1JPAg
Frankreich Lastwagen-Anschlag in Nizza
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Goldsmith

Mutane sama da 80 ne suka rasu bayan da wata babbar mota ta kutsa kai cikin dandazon jama'a a lokacin bikin tunawa da ranar 'yanci a birnin Nice da ke a Kudancin Faransa. Cikin daren ranar Alhamis ne dai da misalin karfe 11 na dare direban wannan babbar mota ya kutsa kai cikin dandazon daruruwan mutane da suka taru a wannan birni dan kallon wasan wuta da aka saba yi a irin wannan rana. Ya dai share kusan tsawon kilomita biyu yana tafiya da motar kan al'umma abin da ya yi sanadi na rayuka mutane da dama da raunata wasu kafin daga bisani 'yan sanda su harbe mutumin bayan da shi ma ya yi amfani da bindiga yana harbi. Shugaba Francois Hollande ya bayyana cewa babu wani dalili na kebe wannan hari daga cikin harin ta'addanci.

Tuni dai wannan hari ya fara samun tofin Allah tsine daga sassa daban-daban na duniya. shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk ya bayyana a lokacin bude taron koli na kasashen Turai da yankin Asiya a Mangoliya cewa kasashen na Turai da ma takwarorinsu na Asiya sun yi Allah wadai da harin na birnin Nice na Faransa.

"Mu bakidayanmu kasashen Turai da yankin Asiya muna tare da al'ummar kasar Faransa da gwamnatin kasar. Mun yi tofin Allah tsine kan wadanda suka haddasa wannan babban abin tashin hankali, za mu ci gaba da hada kai wajen yaki da ta'addanci da ma nuna mummunar kiyayya."

Frankreich Anschlag Soldaten
Jami'an tsaro bayan harin NiceHoto: picture-alliance/AP Photo/C. Fahey