1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama ne suka halarci jana'izar marigayi 'Yar'adua

May 6, 2010

Shugabanni daga ciki, da wajen Nijeriya ne suka halarci jana'izar marigayi shugaba 'Yar'adua

https://p.dw.com/p/NGcg
Hoto: picture alliance/dpa

Mutane da dama ne daga ciki da wajen Nijeriya suka halarci jana'izar marigayi shugaban Nijeriya Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua, wadda aka gudanar a mahaifar sa ta Katsina dake yankin arewacin Nijeriya. Mutane sun yi ta yin kabbara a dai dai lokacin da motar dake ɗauke da gawar ke garzayawa zuwa maƙabartar.

Tawagar gwamnatin Nijeriyar data halarci jana'izar dai, ta kasance ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriyar, Oladimeji Bankole, wadda kuma ta haɗa da 'yan majalisar dattijai dana wakilai, kana da ministoci, da kuma wakili daga sashen shari'ar ƙasar, game da babban sakataren gwamnatin Nijeriyar, Alhaji Mahmud Yayale Ahmad. Hakanan daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar kuma harda tsoffin shugabannin Nijeriya. Da yammacin jiya Laraba ne dai, 'Yar 'adua ya cika, yana da shekaru 58 a duniya bayan da ya yi ta fama da rashin lafiya.

Tuni dai aka rantsar da Dakta Goodluck Jonathan a matsayin shugaban ƙasar - mai cikakken iko. Harkokin siyasa a Nijeriya ya shiga cikin ruɗani tunma gabannin mutuwar marigayin, amma masana na ganin cewar, mutumin daya gajeshi yana da damar yin akin daya kamata - idan har yana da ƙudurin yin hakan, inda suke bada misali da irin kyakkyawar rawar da marigayi Janar Murtala Muhammad ya taka cikin jagorancin sa na watanni shidda kachal.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijjani Lawal