1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun rasu a harin ´yan banga a yankin Niger Delta

January 15, 2006
https://p.dw.com/p/BvC7

Mutane da dama aka halaka lokacin da wasu ´yan bindiga da ake zargi sojin sa kai ne na wata kabila suka kai hari kan wani dandamalin hakan mai dake yankin Niger Delta mai fama da rikici dake kudancin Nijeriya. Hukumomin sun nunar da cewa wasu mutane dauke da manyan bindigogi a cikin kwale-kwale masu gudun gaske sun kai farmaki akan wurin hakan mai na kamfanin Shell dake garin Benisede, sannan daga bisani sun yi musayar wuta da dakarun dake gadin wannan wuri. Rahotanni sun ce an lalata wuraren hakan mai da dama. Birgadiya-Janar Elias Zamani wanda ke jagorantar dakarun dake gadin yankin kudancin Delta ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa ´yan bindiga da kuma sojoji da dama sun rasu a musayar wutar. A ranar laraba da ta wuce wasu ´yan bindiga a yankin na Niger Delta sun yi garkuwa da ma´aikatan mai su 4 dukkansu ´yan ketare.