1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane miliyan goma ne ke fuskantar barazana a Nahiyar Africa

January 16, 2006
https://p.dw.com/p/BvBz

Hukumar bada tallafin abinci ta Mdd, tace kusan dalar Amurka miliyan 240 ake bukata don tallafawa miliyoyin mutane a nahiyar Africa da abinci a cikin wannan shekara.

A cewar hukumar ta Mdd, a yanzu haka akwai mutane kusan miliyan goma da yunwa takewa barazana a wasu kasashe na yammaci da kuma gabashin nahiyar ta Africa.

Hakan , a cewar hukumar bayar da tallafin abincin , ya biyo bayan matsaloli ne na fara da rashin damina mai kyau da kasashen suka fuskanta a shekarar data gabata.

Ya zuwa yanzu dai a cewar rahotanni, hukumar ta Mdd, ta samu tallafin dalar Amurka miliyan 18 da digo hudu daka cikin dala miliyan 240 da take nema.