1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutumin da Paparoma ya naɗa a muƙamin Archbishop na Warsaw yayi murabus

January 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuVB

Sabon archbishop din birnin Warsaw yayi murabus. A cikin wata sanarwa da ya bayar ofishin Fadar Vatikan a Poland ya ce Paparoma Benedict na 16 ya amince da murabus din da Bishop Stanislaw Wielgus ya yi. Da a yau a hukumance aka shirya nadin Wielgus a mukamin na Archbishop a wani taron addu´o´i. Da farko ya amsa cewa ya yiwa hukumar leken asirin Poland a zamanin kwaminisanci aikin leken asiri. Wannan mataki da ya dauka ya zamewa majimi´ar Katholika a Poland wani babban abin kunya musamman a dangane da muhimmiyar rawar da ta taka ta nuna adawa da mulkin kwaminisanci, wanda ya ruguje a shekarar 1989. a ranar 6 ga watan desam Paparoma ya nada Wielgus don ya maye gurbin Cardinal Josef Glemp. Wata sanarwa daga Vatikan ta ce Glemp zai koma kan wannan mukami na wucin gadi.