1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nahiyar Afirka tana makokin John Garang

August 2, 2005

Al'ummar Nahiyar Afrika su na jimamin mutuwar John Garang

https://p.dw.com/p/Bvaf
John Garang
John GarangHoto: dpa

A ranar asabar din data gabata ce mataimakin shugaban kasar Sudan kuma tsohon madugun adawa John Garang ya rasu a hadarin jirgin sama, a yayin da yake kan hanyar sa ta komawa gida bayan ganawar sa da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni. Rasuwar John Garang ta haifar da damuwa ba kawai ga alúmar kasar Sudan, ba har ma da daukacin jamaár gabashin Afrika wadanda suka yi aiki tukuru wajen kawo karshen yakin basasar da ya shafe tsawon shekaru 21 ana gwabzawa tsakanin gwamnatin Sudan da yan tawaye a yankin. John Garang ya jagorancin kungiyar SPLM wajen fafatawa da gwamnatin tare da neman daidaito a tsakanin alúmomin kasar ta kudancin Afrika. Jamaá da dama na ganin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a kudancin Sudan a watan Janairun da ya gabata ba nasara ce kawai ga gwamnatin Sudan ba, amma alama ce da ya nuna cewa alúmomin Afrika na iya warware matsalolin su da kann su Can kuwa a kasar Kenya wadda ta karbi bakuncin taron shawarwarin sulhun inda aka sanya sanya hannu akan yarjejeniyar, jamaá na cike da bakin ciki da alhini na rashin da aka yi .

A ta bakin daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen cimma yarjejeniyar sulhun kuma tsohon jamiín gwamnatin kasar Kenya yace zuciyar sa tana cike da alhini da kuma damuwa musamman kasancewar damar da aka samu ta wanzuwar zaman lafiyar na neman sullibewa.Kasashen Sudan da Kenya da kuma Uganda dukkanin su sun kebe kwanaki uku domin zaman makoki tare da saukar da tutocin kasashen kasa kasa domin girmamawa ga marigayin. John Garang ya sami daukaka da daraja a idanun duniya musamman a kasashen Afrika bisa dattakun da ya nuna da ya kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya hannu akai .

A wata sanarwa shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya baiyana John Garang da cewa mutum ne jan gwaro mai hangen nesa da ya jajirce wajen cigaban alúma, yana mai cewa kasashen Afrika zasu dade suna tunawa da shi bisa kwarjinin sa da kamala da kuma kishin kasa. Alúmomin gabashin Afrika sun sami karsashi da kwarin gwiwa ta wanzuwar zaman lafiya, a yayin rantsar da John Garang a matsayin mataimakin shugaban kasar Sudan, kasar da ya gwabza yaki da ita tun daga shekarar 1983. duban jamaá ne suka yi dafifi a titunan birnin Khartoun a ranar 9 ga watan Yuli, ranar da aka rantsar da Garang a matsayin mataimakin shugaba kasar Sudan .

A cewar wani jakadan kasar Kenya wannan babban abin bakin ciki ne rasuwar John Garang a daidai wannan lokaci, yana mai cewa baki gwiwar su ta yi sanyi. Yace yana fata jamaár kudancin Sudan dama gwamnatin gwamnatin Sudan din zasu aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma domin cigaban wanzuwar lumana da kwanciyar hankali.Wannan dai ita ce damuwar da shi ma shugaban kasar Kenya Mwai kibaki ya baiyana a sakon sa na taáziya ga alúmar Sudan, yace babu wata karramawa da zaá yiwa john Garang face a aiwatar da shirin zaman lafiyar da ya cimma kafin rasuwar sa.Ita ma gwamnatin kasar Habasha ta baiyana rasuwar John Garang da cewa babban rashi ne ga alúmar Sudan dama nahiyar Afrika baki daya.