1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nahiyar Afirka wata daya bayan taron G-8 da bukuwan "Live-Aid-Concert".

YAHAYA AHMEDAugust 1, 2005

Kafin dai a gudanad da taron koli na kasashen rukunin G-8 a Gleneagles din kasar Birtaniya, sai da aka yi wasu bukukuwa a manyan biranen duniya inda shahararrun mawaka suka yi wasanni don janyo hankullan jama'a kan matsalolin da nahiyar Afirka ke huskanta. To ko wane irin sakamako aka cim ma, wata daya bayan shagulgulan taron da bikin da aka yi ?

https://p.dw.com/p/Bvaj
Bikin Live 8 a birnin Berlin, daya daga cikin manayn biranan duniya da suka shirya bikin.
Bikin Live 8 a birnin Berlin, daya daga cikin manayn biranan duniya da suka shirya bikin.Hoto: AP

Kafin taron na G-8 dai, dubbanin jama’a na nahiyar Afirka ne suka sa ran cewa, a wannan karon nahiyar za ta sami damar kubuta gaba daya daga kangin talaucin da take fama da shi shekaru aru aru. Amma wata daya, bayan duk shagulgulan da aka yi na taron kolin kasashen rukunin G-8 a garin Gleneagles da ke Scotland a kasar Birtaniya da kuma bukuwan nan na Live –Aid- Concert da aka gudanar a wasu manyan biranen duniya, me za a iya cewa an cim ma k Mutane da dama na nahiyar dai sun nuna bacin ransu da halin da har ila yau ake ciki, kamar dai yadda wannan dailbar ta birnin Johannesburg ta bayyanar:-

„Babu wani sauyin da aka samu tun wannan babban shagalin – sam babu abin da ya canza.“

Wata mace kuma ta bayyana ra’ayinta ne kamar haka:-

„Kome ma sai kara tabarbarewa ya yi. Shugabannin kasashen G-8 dai ba su damu da nahiyar Afirka ba. Suna fama ne da kasashensu, babu abin da ya dame su. Romon baka kawai suke yi, don su nuna wa duniya cewa suna da kyakyawar manufa ga nahiyar Afirka. Amma a zahiri babu wani abin a zo a ganin da nahiyar ta samu. Haka kuma za a ci gaba da tafiya.“

A galibi dai, mafi yawan jama’a sun bayyana takaicinsu game da abin da suke gani kamar cikas ne, bayan duk kururuwan da aka yi ta yi wajen tallata taron na Gleneagles. A duk muhimman batutuwan da aka tattauna a kansu, wato nuna adalci a harkar kasuwanci da Afirka, da yafe wa kasashen nahiyar basussukansu, da ba da isashen tallafi wajen yakar cutar nan ta AIDS da kuma taimakon raya kasa, babu wata fa’idar da nahiyar ta samu.

Quinton Mageza, na daya daga cikin wadanda suka hirya bikin Live-Aid-Concert din a birnin Johannesburg. A nasa ganin dai:-

„Babban abin ban takaici shi ne rashin cim ma wata muhimmiyar yarjejeniya kan huldodin cinikayya da kasashen nahiyar. Har ila yau, kasashen rukunin G-8 din sun dage ne kan tsoffin manufofinsu na jari-hujja, wadanda kuma suke son kowa ya bi, wato na sayad da jarin kamfanonin da ke hannun gwamnati, da janye shirin kayyade farashi da kuma kau da shingen kare kasuwannin kasashe matalauta.“

Wato a zahiri, har ila yau, bankin duniya, kafin ya bai wa wata kasa ta Afirka rance, zai iya jibinta rancen da wasu sharuddan da ya kamata a cika, kamar bude kasuwannin Afirkan ga wasu kayayyaki daga nahiyar Turai. Sakamakon haka kuwa shi ne, sai a sami ambaliyar kayayyaki daga Turai, wadanda gwamnatocin kasashen Turan suka zuba musu karo don farashinsu ya yi kasa. To wadannan kayayyakin kamar dai na albarkatun gona, sai su karya darajar kayayyakin gonar da manoman nahiyar suka noma. A lal misali haka ne dai ya auku a kasar Ghana, inda gwangwanin tomatir daga kasar Holland ya fi na wanda aka sarrafa cikin kasar rahusa.

Taron na rukunin kasashen G-8 dai, bai warware matsalar batun zuba karo ga kayayyakin noma da kasashe mawadatan ke yi ba. An dai yi musayar yawu ne kawai kan batun. Amma ba a tsai da takamaiman lokacin da za a fara daukan matakai don shawo kan matsalar ba. Masu sukar lamiri kan al’ammuran da suka shafi nahiyar dai na ganin cewa, yafe bashin dola biliyan 40 da aka yi wa wasu kasashen nahiyar bai wadatar ba.

Kamar yadda Mageza ya bayyanar:-

„Wannan matakin dai ba zai warware matsalar ba a zahiri. Abin da zai fi ma’ana shi ne soke bashin dola biliyan 15 zuwa 20 a ko wace shekara. A ganina dai, an rufe wa Afirka kofar samun sassauci ne kafin ma ta yunkuri shigarta.“

A takaice dai, jama’an Afirkan da dama na ganin cewa shugabannin kasashen rukunin G-8 din, ba kawai don suna sha’awar ganin Afirka ta kubuta daga kangin talauci ne suka yi wannan taron ba. Sabili da haka ne masu fafutukar neman samun adalci a harkokin ciniki a duniya suke bayyana ra’ayin cewa, ya kamata a ci gaba da gudanad da zanga-zanga don angaza wa shugabannin kasashe mawadatan. Suna dai tinkarar gudanad da zanga-zanga ne a taron Majalisar dinkin Duniya da za a yi a cikin watan Satumba mai zuwa don yin nazari kan irin sakamakon da aka samu wajen aiwatad da shirye-shiryen wannan karnin da majalisar ta gabatar a cikin shekara ta 2000.