1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An dakile harin ta'addanci

Ramatu Garba Baba
December 26, 2017

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewar ta yi nasarar dakile wani yunkurin mayakan kungiyar Boko Haram na kai hari a birnin Maiduguri da ke a Jihar Borno a yayin da jama'a ke tsakiyar gudanar da bukukuwan KIRISMETI.

https://p.dw.com/p/2pwQw
Nigeria Kampf gegen Boko Haram | ARCHIV
Hoto: picture alliance /AP Photo/L. Oyekanmi

Dakarun sojin Najeriya sun yi musayar wuta da mayakan na Boko Haram a lokacin da suka doshi wani shingen bincike a motocinsu kirar a kori kura inda a nan ne sojojin suka mayar da martani suka kuma yi nasarar fatatakar mayakan a cewar wani babban hafsan sojin rundunar sojin ta yankin arewa maso gabashin kasar Nicholas Rogers. Duk da cewar ba a samu asarar rai ba bisa nasarar da aka samu kan mayakan, an karfafa tsaro a duk fadin yankin da ya sha fama da ayyukan kungiyar. Mutane fiye da miliyan biyu rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu baya ga dubban da suka rasa rayukansu a shekaru takwas na ayyukan kungiyar ta Boko Haram a Najeriya.