1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An yi gyara a dokokin zabe

Uwais Abubakar Idris
March 31, 2017

A matakin da ake ganin muhimmin sauyi ne a dokar zaben Najerya majalisar dattawan kasar ta amince da gyaran dokar zabe da ta halasta amfani da tsarin jefa kuri’a ta amfani da na'ura mai aiki da kwakwalwa.

https://p.dw.com/p/2aSAy
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Wannan dai shi ne karon farko da aka yi muhimman sauye- sauye a dokar zaben Najeriya da majalisar dattawan kasar ta amince da ita, a matakin da a zahiri ke nuna kan mage na kara wayewa a game da batun zabe da ma masu tunanin tafka magudi da sannu a hankali ake toshe hanyoyin na zahiri da aka sani na magudin zabe a tarayyar ta Najeriya.

Wahl Nigeria Abuja
Hoto: DW/Uwaisu A. Idris

Domin amincewa ga hukumar zaben kasar ta yi amfani da na'ura mai aiki da kwakwalwa wajen jefa kuri'a maimakon wanda aka saba da shi na baiwa masu jefa kuri'a takarda su dangwala jamiyyar da suke so a lokacin zabe, duka matakai na kyautata zaben Najeriyar. Majalisar dattawan ta kuma amince da amfani da na'ura mai aiki da kwakwalwar wajen tattrarawa da aikawa da sakamakon zabe da zarara an kamala maimakon jiran sai an dauko shi a mota inda a mafi yawan lokuta a kan samu matsaloli na zargin aringizon kuri'a. Wannan ya zo dai dai da abin da hukumar zaben ta dauka tare da amincewa da shi. Ko hukumar zaben a shirya ga wannan sabon tsari da yake sabo fil ga daukacin tsarin zaben Najeriyar?  Mr. Nick Dazang darakta ne a sashin yada labaru na hukumar zaben Najeriyar ya ce sun shirya tsaf dan wannan aiki kamar yadda aka ga aiyukansu a baya.

Tuni dai ‘yan siyasa suka mayar da murtani a kan wannan sabon tsari da aka dade ana jiran ganin faruwarsa musamman sanin bukatar kyautatawa da ma inganta yanayin zaben kasar.