1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Boko Haram ta sace yara 1000

Ramatu Garba Baba
April 13, 2018

Asusun kula da ilimin kanana yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce, fiye da yara 1000 ne mayakan Boko Haram suka sace a Najeriya, tun daga shekara ta 2013 ya zuwa yanzu da ayyukan kungiyar ke kara tsananta.

https://p.dw.com/p/2w1tB
Nigeria Demonstration gegen die Entführung von Schulmädchen
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Cikin wannan alkaluman da Asusun ya fitar, har da 'yan matan sakandaren garin Chibok 276 da aka sace a shekara ta 2014. An tattaro alkaluman ne bisa bayanan da aka samu ko kuma wadanda aka sanar da labarin batansu. Wannan na zuwa ne a yayin da ake shirin taron tunawa da sace 'yan matan garin na Chibok shekaru hudu da suka gabata a jahar Borno, da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Akwai malaman makaranta dubu biyu da 295 da suka rasa rayukansu acewar Asusun, kuma har yanzu ba a daina kai hare-hare ko sace-sacen yara a yankin ba, lamarin da Asusun na UNICEF ya baiyana hakan da wani abin takaici ga irin barazanar da rayuwar yara kanana ke fuskanta a Najeriya.