1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce bayan korar dan majalisa

September 29, 2016

A Najeriya kungiyoyin rajin yaki da cin hanci sun maida martani a game da dakatar da Hon Abdulmumini Jibril da majalisar wakilai bisa tona asirin zargin shugaban majalisa na arangizo kudi sama da biliyan 200.

https://p.dw.com/p/2QkNP
House of Representatives in Nigeria
Hoto: CC BY-SA 2.0

 
Dakatar da Honorable Abdulmuminu Jibril da majalisar wakilan ta yi bayan  bankado zargin aringizo a kasafin kudin na wannan shekara da ya yi wa shugabanin majalisar bayan da suka raba gari da ma bukatar da ya yi ta lallai a gudanar da bincike ya sanya kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar maida martani.
Majalisar da ta dage a kan ya karya ka'idojin majalisa ba tare da duba zargin da ya yi mata da aringizo a kasafin kudin ba ya sanya Barrister Mainasara Umar mai fafutukar yaki da cin hanci bayyana cewa akwai abin dubawa.


"Kyale jaki ne aka yi ana bugun ba ma taikin ba ,kayan da ke cikin taikin ake nema a buga an kyale jaki, sabo da abin da ya kamata a yi shi ne ita majalisa ta yanke cewa tunda mu ne ake zargi, to muna kira ga hukumomi na kasa su zo su bincika"


Bankado zargin na rub da ciki a kan kudadden jama’a dai muhimmin mataki ne ga yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, amma rashin kariya ga dimbin ‘yan Najeriya na cikin bukatun da kungiyoyin farar hula suka dade da nuna bukata, ko wace illa wannan zai yi ga masu irin wannan hali? Mr Kola Banwo jigo ne a kungiyyar Ciislac da ke yaki da cin hanci da sanya idannu a ayyukan ‘yan majalisa.

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba


" Dole in za a yi yaki da rashawa a nan kasar ya kamata mu samu doka. In ba doka doli zai wuya a samu masu fadin gaskiya in kowa ya san za a kore shi daga aiki ko zai samu wata matsala, kara ya yi shiru. shi ya sa mun ce wannan gwamnati da ta zo in tana so ta yi yaki da cin hanci da gaskiya to ta kafa doka"


Matakin da majalisar ta dauka a kan Hon Abdulmuminu Jibril da suka hada da hana shi rike duk wani mukami har karshen majalisa ta takwas baya ga dakatarwa na shekara guda ya sanya wasu yan majalisar nuna adawa. Hon Gudaji Kazaure na mai cewa.


"Wannan hukunci na yi kokarin in tsai da shi kafin a yi shi domin akwai irin wannan rikici a majalisar dattawa wanda har sun kai shugaban majalisar kotu wanda bai dakatar da kowa a cikinsu ba sai ma jawosu ya yi a jiki. Sannan abin da ya bani haushi shi ne shekara daya wai zai wakilci Kiri da Bebeji? Dokar kasa ta yarda da wannan? Abin da yake zargi inda ya kai takardu wajen IFCCda sauransu sun karyata shi ne"

Nigeria Plakate und Aufkleber gegen Korruption
Hoto: DW/K. Gänsler


To sai dai ga Hon ….. yace suna da hujjar daukan wannan mataki.


"An yi adalci a cikin abubuwan na cewa Abdulmumuni Jibril ya tafi ya gyara halayansa"


Abin jira a gani shi ne matakin da kotu za ta dauka a kan karara da Hon Abdulmuminu Jibril zai shigar don kalubalantar korar tasa daga majalisa a wannan badakala da shi ne karon farko da wani dan majalisa ya bankado zargi na aringizo a kasafin kudi a kan shugabanin majalisa a Najeriyar.))