1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce kan tallafin yaki da Boko Haram

December 15, 2017

'Yan Najeriya na gudanar da zazzafar muhawara kan matakin da kungiyoyin gwamnonin kasar suka dauka na bai wa gwamnati dala bilyan daya domin yaki da ayyukan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/2pRXP
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari und die freigelassenen Chibok-Mädchen in Abuja
Hoto: Reuters/Presidential Office/B. Omoboriowo


Kungiyar gwamnonin Najeriya ta sanar da wannan mataki na a ciro kudi daga asusun rarar mai bayan kammala taro na majalisar zartarwa da nufin kashe kudaden saboda yadda su ka gamsu da ci gaban da aka samu a yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar inda suka yi imanin samar da kudaden don kawo karshen rikicin na shekaru da dama. Amman matakin ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan kasar dangane da wannan mataki da nasarar da gwamnonin ke ikirarin an samu da har zai kai ga amincewa gwamnatin tarayya kashe wadan na makudan kudade musamman ganin yadda ake samun sabbin hare-hare daga mayakan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.


Yayin da wasu ke ganin amincewa da kashe makuden kudin don yaki da Boko Haram zai bada dama kawai ga wasu su sami damar wawashe kudaden kamar yadda aka yi a  baya wasu kuma yabawa suka yi saboda a cewar su hakan zai sa a biya jami'an tsaro hakkokin su abinda zai karfafa musu guiwa su ci gaba da yaki don kawo karshen matsalar tsaro.Wasu bangaren kuma tambaya suka yi kan kudaden da a abaya aka ware da sunan yaki da ta'addanci da ma kudaden da ake warewa duk shekara da sunan tsaro. Matsalar tsaro da rikicin Boko Haram ta haifar na ci gaba da zama barazana a shiyyar arewa maso gabashin kasar, inda kungiyar ke kara kai hare-haren a kauyuka da kuma na kunar bakin wake lamarin da ya yi sanadiyyar rayukan fararen da dama.