1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cikas a musayar 'yan Chibok

Yusuf BalaSeptember 17, 2016

Da yake jawabi ga manema labarai ministan yada labarai Mista Lai Mohammed ya ce dakarun tsaro na farin kaya sun shiga tattaunawa da mayakan tun daga watan Yuli na shekarar 2015.

https://p.dw.com/p/1K47g
Screenshot mutmaßliches Boko Haram Video
Mayakan na Boko Haram dai sun ce sai an saki dakarunsu kafin su saki 'yan ChibokHoto: youtube/Fgghhfc Ffhjjj

Gwamnatin Najeriya ta bude kofa ta tattaunawa da mayakan Boko Haram a kokari na ganin an sako yara 'yan Makarantar Chibok tun a shekarar 2015, sai dai kawowa yanzu shirin ceton yaran na fiskantar tangarda saboda rabuwar kai a tsakanin mayakan na Boko Haram a cewar ministan yada labarai a Najeriya.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja fadar gwamnatin ta Najeriya Mista Lai Mohammed ya ce dakarun tsaro na farin kaya sun shiga tattaunawa da mayakan tun daga watan Yuli na shekarar 2015 a kokari na ganin an yi musayar yaran sama da 200. Sai dai gwamnati ta rufe ci gaba da batun a watan Agusta 2015 bayan da mayakan suka bijiro da wasu sabbin bukatu. A watan Nuwamba an sake komawa kan tattaunawar sai dai rikicin shugabanci a kungiyar ya maida hannun agogo baya.

A cewar Lai Mohammed duk da tangarda gwamnati na kokari na ganin ba ta karaya ba a kokari na kubutar da 'yan matan bayan da ake samunci gaban tuntuba ta wadanda gwamnati ta amince da su.