1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Dawowar Shugaba Muhammadu Buhari daga London

Salissou Boukari
March 16, 2017

Jirgin da ya dauko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari daga birnin London ya sauka a filin jiragen sojoji na Kaduna.

https://p.dw.com/p/2ZJv8
Afrika Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya dowo gida Najeriya daga LondonHoto: Reuters/Stringer

Bayan da jirginsa ya sauka a Kaduna sakamakon rufe filin jiragen sama na birnin Abuja domin ayyuka, Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi zuwa Abuja cikin wani jirgi mai saukar ungulu, inda manyan jami'an gwamnati da ma gwamnoni suka yi masa babban tarbo cikin nuna farin ciki da dawowar shugaban.