1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ganawar shugaban kasa da majalisa

Ubale Musa | Lateefa Mustapha Ja'afar
April 3, 2017

A Najeriya shugaban kasar da kuma shugabannin majalisun dattijai da wakilai, sun tattauna na tsahon wuni guda da nufin kawo karshen takaddamar da ke tsakanin majalisar da bangaren zartaswa.

https://p.dw.com/p/2abFc
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Reuters/A.Akinleye

An dai kai ga share tsawon makon jiya ana tafka wa a tsakanin 'yan majlisar tarrayar Najeriyar da ke fadin ko mutuwa ko yin rai, da kuma fadar shugaban kasar da ke kiran hanci na neman mai da martani a yakin da yake fuskanta. To sai dai kuma an shiga sabon mako tare da bangarorin guda biyu suna shirin yasar da makamai domin sulhun da ke da tasirin gaske a cikin harkoki na kasar. Wani rikicin da ke kama da na isa ne dai, ya nemi rusa daukacin tsari na gwamnatin kasar, kafin daga baya hankali ya koma a jiki bayan da talakawa suka fara daukar matakin ba sani ba kuma sabo da ya kai har ga jifan wasu a cikin 'ya'ya na majalisar dattawan. Ana dai kallon sulhun da ya kalli hadin gemu a tsakanin shugaban kasar da sakatare na gwamnati sannan kuma da shugabannin majalisun dattawa da wakilai, a matsayin abun da ke iya kai wa ga bude sabon babi a tsakanin zartarwar da y'an uwansu 'yan doka, da a cewar shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ke da tunani iri guda game da makoma ta kasar. #b#

Jan aikin da ke gaba

Jam'yyar APC mai mulki a Najeriya
Jam'yyar APC mai mulki a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

To sai dai kuma ko ya zuwa ina tabbacin na saraki ke iya kai wa ga kwantar da hankula cikin kasar dai, jan aikin na zaman sakkowa daga dokin nakin na majalisu, tare da kai wa ga mika wuya ga jeri na bukatu na gwamnatin. An dai kai ga ruwaito daya a cikin jami'ai na gwamnatin na ta'allaka rikicin da kokari na manya na barayi na kasar, na mai da martani ga yakin hancin da take yi a halin yanzu. Karatun kuma da a cewar Abdurahaman kawu Sumaila da ke bada shawara ga shugaban kasar bisa harkoki na majalisar babu gaskiya ko ta kalilan a ciki. Abun jira a gani dai na zaman tasirin sulhun a kokarin kasar na kai wa ga tudun muntsira, da kila samar da ci-gaban da 'yan kasar ke fata su gani a kasa.