1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Goyon baya ga Shugaba Muhammadu Buhari

August 14, 2017

Dubban magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari sun gudanar da zanga-zanga domin jaddada goyon baya a gareshi, a wani abun da ke zaman yunkuri na dakushe adawa da zamansa a birnin London.

https://p.dw.com/p/2iCHv
Muhammadu Buhari speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos, Nigeria
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Reuters/A.Akinleye

Duk da cewar har za yuwa yanzu bai kai ga saukar ba, darururwa na magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari daga dukkan alamu sun sauka da kwari daga sassa dabam-dabam na arewacin kasar domin zanga-zanga ta nuna goyon bayan shugaban na Najeriya. Kama daga can kauyensu a Daura ya zuwa birnin Abuja da ma sassa dabam-dabam na arewa, matasa da kuma dattawa mata da maza sun cika dandali na Unity Fountain da ke Abuja domin zanga-zangar da ke zaman irinta mafi girma da kuma ke da nufin aiken sako ga masu ikirarin ganin sai shugaban ya yi murabus.

Zaman Shugaba Buhari a London na janyo cece kuce

Nigeria Muhammadu Buhari in London
Lokacin da tawagar Gwamnonin APC suka ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a LondonHoto: Reuters/Nigeria Presidency

Ko bayan nasarar tarwatsa taro na masu adawa da Buharin da suka mai da dandalin wajen cin karensu har gashinsa, magoya baya na Buharin dai sun ce sun zo da nufin shaida wa duniya goyon baya ga Buharin da a fadar da damansu ya kai ga sauya rayuwa ta da dama. Ko bayan imani da rayuwa da halayya ta Buharin dai daga dukkan alamu wani abun da ya dauki hankalin masu goyon bayan na zaman rawa da gwamnatin ke takawa wajen yaki da cin hanci da kuma kai karshen tasirin harkoki na 'yan Boko Haram da a baya suka gagari kundila.

Goyon baya da adawa tsakanin Kudu da Arewa

Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Masu zanga-zanga a NajeriyaHoto: dapd

Wani abun lura ga masu zanga-zangar soyayya da kuma adawa da Buharin dai na zaman rabuwarsu tsakanin arewacin kasar da kudancinta. A yayin da kusan kaso 95 cikin 100 na masu neman kyale Buhari ya huta sun zo daga arewa, masu kokarin kai karshen mulkin nasa na zaman na sashen kasar da ke kudu a wani abun da ke zaman alamun rabuwar da har yanzu ke tsakanin manyan sassa na kasar guda biyu.