1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gwamnan Filato ya soki dokar hana kiwo

January 11, 2018

A wani mataki na nuna sabani kan batun rikin manoma da makiyaya a Najeriya, gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya soki matakin gwamnonin Benue da Taraba na kafa dokar hana kiwo ba tare da yin adalci ba.

https://p.dw.com/p/2qi8T
Nigeria Konflikt Farmer Pastoralisten
Kiwo na makiyaya na haddasa tashin hankali a wasu jihohin NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Har ya zuwa yanzu dai ana kirga asara a lunguna da sakuna na tsakiyar Tarrayar Najeriya, har kuma yanzu zuciya tana numfasawa a game da rikicin makiyaya da manoman da ke neman rikidewa ya zuwa na siyasa. To sai dai kuma har a tsakanin shugabannin yankin da wannan rikici ya fi kamari ana kara samun rabuwar kawuna game da dokar hana kiwon da ke zaman musabbabin rikicin da ke kara tada hankali. Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya ce ba hujjar kafa dokar tun da farkon fari ba tare da tabbatar da samar da hanyoyi na aiwatar da ita.

Flash-Galerie Tuareg
Makiyaya masu kiwon shanu na fuskantar kalubaleHoto: AP

Gaggawa a cikin mulkin jama'a ko kuma kokari na cika buri a siyasa dai,  a yayin da ake kirga asara a jihohin na Benue da Taraba dai an kamalla bukukuwan kirisimeti da na sabuwar shekara lafiya da kwanciya ta hankali a jihar Filato da a baya take zaman cibiyar rigingimu makamantan wannan. To sai dai kuma  babban sirrin a fadar Gwamna Lalong na zaman rungumar daukacin al'umma ta Filato a cikin halin adalci a tsakanin kowa. Ana dai kallon sabon rikicin da ya dauki launi irin na banbancin kabila da kila ma na addini a cikin yankin ka iya rikidewa ya zuwa na siaysa ga kasar da ke kara tunkarar lokaci na zabuka.