1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iska ta haddasa asara a jihar Bauchi

Aliyu Muhammad Waziri
June 19, 2018

Sama da mutane 80 sun mutu a yayin da gidaje da dukiya masu yawa suka salwanta a sanadiyar iska mai tsananin da ta afka a wasu yankunan Bauchi.

https://p.dw.com/p/2zqoi
Yadda guguwar iska ta haifar da ta'asa a Nijar
Yadda guguwar iska ta taba haifar da ta'asa a Nijar Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Bala'in iskan ya rusa gidajen jama'a da dama yayin da sama da mutane 300 suka jikkata, akalla gidaje 1230 ne suka lalace. Iftila'in dai shi ne irinsa na farko a tarihin jahar.

Tun bayan aukuwar wannan lamarin, gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamiti wadda zai zaga ya kuma duba irin barnar da wannan iska ta yi a cikin garin Bauchi da kewaye. Unguwar Kobi da ke a tsakiyar cikin garin Bauchi ta na daya daga cikin wuraren da wannan masifa ta fi shafa inda shagunan 'yan kasuwa da dama suka ruguje. Tuni gwamnan Jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ya mika sakon ta'aziyyar sa ga wadanda wannan masifa ta shafa.