Najeriya: Karuwar mutuwar yara a Arewa | Zamantakewa | DW | 05.12.2017

Zamantakewa

Najeriya: Karuwar mutuwar yara a Arewa

A Najeriya wata kididdigar hadin gwiwar Hukumar UNICEF da hukumar kididdiga ta kasa, ta nuna yadda ake samun karuwar mace-macen kananan yara 'yan kasa da shekara biyar a yankin Arewa maso Gabas.

Hungersnot in Nigeria (picture alliance/dpa/Unicef/NOTIMEX)

 

Kididdigar ta nunar da cewa duk cikin yara goma da aka haifa, yaro daya kan rasa ransa cikin kwanaki biyar da haifarsa, sannan cikin dari da ake haifa, bakwai suna zuwa ne a mace. Dr. Danjuma Almustapha shi ne jami’in tsare-tsare na hukumar UNICEF ta shiyyar Arewa maso Gabas.


Sai dai kuma yayin da adadin mace-macen yaran ke karuwa a yankin Arewa maso gabashin Najeriyar, adadin raguwa yake a yankin Kudu maso kudancin kasar inda alkaluman binciken suka yi nuni da cewa kimanin yara162 ne ke mutuwa a duk cikin yara dubu daya wadanda suke kasa da shekara biyar. Har ila yau binciken ya bayyana karancin rigakafi ga kananan yara daga cikin ababen da suke haddasa karuwar matsalar kamar yadda babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Bauchi Dr. Sa’idu Aliyu Gital ya bayyana

NIGERIA Hunger und Mangelernährung (Getty Images/AFP/F. Plaucheur)

.


Yayin gabatar da rahoton wannan bincike dai, jami’ai daga jihohi shida na Arewa maso gabashin Najeriyar da suka hada da Adamawa, Borno, Bauchi, Gombe, Yobe da Taraba sun halarci wurin har ma kuma sun nuna gamsuwa da abin da binciken ya kunsa, suna masu fatan daukar matakan da suka dace don magance wannan matsala.


Binciken ya tabo batun karancin shayar da nonon uwa zalla, hadi da rashin abinci mai gina jiki daga cikin ababen dake taimakawa gaya wajan karuwar mace-macen yaran.

Albanian Shqip

Amharic አማርኛ

Arabic العربية

Bengali বাংলা

Bosnian B/H/S

Bulgarian Български

Chinese (Simplified) 简

Chinese (Traditional) 繁

Croatian Hrvatski

Dari دری

English English

French Français

German Deutsch

Greek Ελληνικά

Hausa Hausa

Hindi हिन्दी

Indonesian Bahasa Indonesia

Kiswahili Kiswahili

Macedonian Македонски

Pashto پښتو

Persian فارسی

Polish Polski

Portuguese Português para África

Portuguese Português do Brasil

Romanian Română

Russian Русский

Serbian Српски/Srpski

Spanish Español

Turkish Türkçe

Ukrainian Українська

Urdu اردو