1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Miyetti Allah ta maida martanin zargin 'ya'yanta

Uwais Abubakar Idris/ YBMay 2, 2016

Abin da ya fi daga hankalin al'umma shi ne irin muggan makaman da ake ambato cewa Fulanin na amfani da su wajen kai hare-hare.

https://p.dw.com/p/1Igjz
Niger Agadez Afrika
Bafulatana da dabbobi a bakin ruwaHoto: picture-alliance/Bildagentur-online/Hermes Images

To wannan rikici da ake danganta shi da zargin Fulani makiyaya da ke watsuwa zuwa sassan Najeriyar dai a yanzu ya zama wanda ake ci gaba da yamadidi a kansa musamman harin baya-bayan nan da aka kai a garin Enugu, abin da ya sanya shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari bai wa hukumomin tsaro umurnin shawo kan matsalar.

Kungiyar Miyetti Allah ta Fulanin da ta maida martani a kan lamarin tana mai cewa tana goyon bayan matakin gwamnati amma fa dora laifin kacokan a kan duk wata kabila ba zai yi wa Najeriyar kyau ba. Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru shi ne shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta Najeriyar.

Nigeria Normaden Fulani Hütten bei Abuja
Wasu Fulani a wani yanki na AbujaHoto: dapd

"Maganata ko yaushe ana danganta Fulani da aiyukan ta'adanci ba abu ne da zai haifar wa kasa da mai ido ba, amma mu muna goyon bayan matakin da gwamnati ta dauka na a gano masu aikata wannan laifi, domin rashin hukunta su ya sanya muka kai halin da muke ciki."

Munin wannan lamari dai tuni ya sanya majalisar dattawan Najeriya shiga cikin lamarin ta hanyar tsawatarwa da ma bukatar lallai a yi bincike don gano bakin zaren maimakon shasshafa shi da a kan yi. Sanata Ali Wakili dan majalisar dattawan Najeriya na mai bayyana cewa:

A young fulani herdsmen
Matashin Bafullace a kan aikin kiwoHoto: DW

"In aka dubi al'ummar Fulanin nan za a ga cewa ba ainihin Fulaninmu da muka sani ba ne, ai Fulaninmu za ka same su da sandarsu da gorarsu, amma wadannan suna rike da bindigogi ne fa, su kansu kashe Fulanin suke yi, don haka ya kamata a yi taka tsan-tsan."

Masana a harkar tsaro dai na ganin cewa wannan lamari abu ne da ke bukatar yin taka tsantsan da zurfafa bincike ganin yadda matsalar ta tsaro da ta gallabi kasar ta Najeriya da makotanta.