1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kungiyoyi na son zama jam'iyyu

March 15, 2017

A wani abun da ke iya kaiwa ga karin rudani a cikin fage na siyasar Najeriya, akalla kungiyoyi na siyasa 86 ne dai suka mika takardar neman rikidewa ya zuwa jam'iyyu a fadar hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC.

https://p.dw.com/p/2ZE7A
Wahlkampf in Nigeria 2015
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Sannu a hankali dai suna kara yawa cikin kasa, sannu a hanakali kuma suna neman kasa biyan bukatar al'umma ta kasar, ga jam'iyyu na siyasa a cikin Najeriya da suke shirin kara yawa daga 54 zuwa sama da dari a halin yanzu.

Wata sanarwar hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC dai ta ce akalla kungiyoyi na siyasa 86 ne suka mika bukata ta neman rikidewa ya zuwa jam'iyyu da nufin taka rawa a fage na siyasa ta kasar mai tsidau da karangiya.

Parlamentswahl 2011 in Kano State Nigeria
Hoto: DW

Kundin tsarin mulki na kasar dai ya tanadi yin rijista ta siyasa ga duk wani mai bukata da zarar ya cika sharadin kama ofishi a babban birnin tarraya na Abuja.

Duk da cewar dai hukumar zaben kasar ta yi nasarar soke rijistar wasu jam'iyyu na kasar dai dai har 10 bayan kammala zabukan kasar na shekara ta 2015, wani hukuncin kotu ya tislata wa hukumar zaben mayar da rijistar da ta ba su damar cigaba a matsayin jam'iyyu da ke iya taka rawa yayin zabe a kasar.

Dr. Umar Ardo dai na zaman wani dan siyasa a kasar da har ila yau kuma ke sharhi a bisa lamuran na siyasar Najeriyar, a fadarsa karuwa ta yawan jam'iyyun na zaman alamar rabuwar kawuna ta 'yan kasar bisa buri na tara abun duniya maimakon hidima ta 'yan kasa. To sai dai kuma a fadar Alhaji Mohammed Lawal Nalado da ke zaman shugaban jam'iyyar Accord kuma shugaban gamin gambizar jam'iyyu na kasar, su kansu kananan na da rawar takawa in har an tabbatar da adalci a cikin filin wasan.