1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Majalisa ta amince da kasafin 2017

Uwais Abubakar Idris
May 11, 2017

‘Yan majlisun dokokin Najeriya sun amince da kasafin wannan shekara ta 2017 na sama da Naira tirliyan bakwai da digo hudu, bayan fuskantar jinkiri, inda a karon farko majalisar da kanta ta fitar da kasafin kudinta.

https://p.dw.com/p/2cp8Z
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki shi ya jagoranci 'yan majalisar wajen amincewa da kasafin kudin na wannan shekara. Kasafin kudin da Shugaba Buhari ya mika wa majalisar a ranar 16 ga watan Disamba mai taken kasafin kudin farfadowa da bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ‘yan majalisar sun tsara shi ne bisa sa ran samun hako mai ganga milyan 2.2, to sai dai ‘yan majalisar sun dora farashin na man fetir daga Dala 42.5 da shugaban Najeriyar ya gabatar zuwa Dala 44.5 a kan kowace gangar man fetir.

Sanata Barau Jibril na majalisar datawan Najeriya ya bayyana muhimman abubuwan da ke kunshe a kasafin kudin na wannan shekara, inda ya ce tsari ne da ba a taba yi ba.

A majalisar wakilan Najeriyar ma ‘yan majalisar sun amince da kasafin kudin bisa wannan adadi da ya nuna cewa duka majalisun biyu sun yi kari a kan abin da shugaban Najeriyar ya gabatar. A karon farko sashin gudanar da muhimman ayyuka ya samu kashi 30 cikin 100 wanda  shi ne kaso mafi tsoka  da aka baiwa sashin a 'yan shekarun nan, abi nda ya nuna sama da Naira tirliyan biyu aka kebewa sashin. Ko me suka hango suka yi wannan sauyi?  Hon Sidi Yakubu Karasuwa ya ce a bana talaka zai dara.