1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Makomar Boko Haram bayan karbe Sambisa

December 27, 2016

'Yan kwanaki da sanar da kame dajin Sambisa daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram makoma ta mayakan kungiyar na cigaba da daukar hankalin masu ruwa da tsaki a yakin arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2Uvfo
Boko Haram
Hoto: Java

A cikin karshen mako ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ga sanar da cewar dakarun kasar sun karbe iko da babbar tungar 'yan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno, inda aka kame da dama a cikin 'yan kungiyar. Duk da cewar dai har ya zuwa yanzun babu dalla-dalla na irin nasara ta gwamnatin balle sanin makomar jagorori na bangarori na kungiyar guda biyu, sanarwar ta shugaban kasar dai ta bude sabon babi a cikin yakin na shekaru kusan bakwai. Tuni dai sojan kasar suka ce sun nasarar kassara karfi na kungiyar tare da gargadi ga 'yan kasar na taka-tsantsan kan irin abinda za su iya aikatawa idan suka shiga cikin mutane suka saje da su.

Nasarar kame dajin na Sambisa dai na nufin cika daya daga cikin uku na alkawura na shugaban kasar bayan zabe, abun kuma da a cewar Isa Tafida mafindi da ke zaman dan jam'iyyar APC ta shugaban kasar ya ishesu yin alfahari a yanzu. To sai dai duk da wannan alfahari da APC din ke yi sakamakon wannan nasara da ta ce ta cimma, daga dukkan alamu har yanzu akwai sauran tafiya dangane da kawo karshen wannan matsala da ta jawowa kasar kalubale babba ta bangaren tsaro.

A baya dai kasar ta sha murkushe rikici mai kama da Boko Haram din amma kuma lamura suka sake dagulewa, abin kuma da ya sanya masana yin kira ga hukumomi da lallai su tabbata sun kawo karshen matsalar baki dayanta sai dai yayin da gwamnatin ke kokari wajen ganin ta tabbatar da tsaro a yankin, wasu na ganin da wuya 'yan Boko Haram din su iya wani tasiri na kirki a jihar ta Borno da ma sauran sassan da rikicinsu ya mamaye.