1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsalar kasafin kudin shekarar bana

October 4, 2017

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce tana shirin tura mafi yawan kasafin zuwa badi saboda mummunar matsalar rashin kudi da ake fuskanta a kasar.

https://p.dw.com/p/2lDim
Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Hoto: Getty Images

Al'ummar tarrayar Najeriyar  da gwamnatin kasar dai sun dauka daga bana kasar za ta yi nasarar daukar harami, sakamakon kasafin da ke zaman irin sa a farko da kuma yake fatan dorawa a cikin aikin ginin kasa da samar da ababe na more rayuwa.To sai dai kuma kasa da watanni uku da kai karshe ga shekarar dai daga dukkan alamu tana shirin baki ga kasar da ta ce ba ta da kudin ci gaba da aiwatar da sama da rabin kasafi na manya na ayyukan kasar.

Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Abin kuma da ya tilasta wa majalisar dattawa ta kasar wani sammaci na musamman ga ministocin da ke da ruwa da tsaki da aiwatar da kasafin kudin kasar na bana domin jin halin da ake yanzu akalla watanni Hudu bayan rattaba hannu kan kasafin. Ministan kudin kasar Kemi Adeosun dai ta shaida wa dattawan cewar  akalla kaso 60 a cikin dari na kasafin na manya  ayyukan kasar za su kaishi a shekarar badi.