1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Muhawara kan yarjejeniyar cinikayya ta Afirka

March 20, 2018

Shugabannin kasashen nahiyar Afirka na gudanar da taro a birnin Kigali na kasar Ruwanda don tattaunawa kan batun samar da kafa ta inganta fannin cinikayya a tsakanin kasashen, matakin da Najeriya ke dari-dari kansa.

https://p.dw.com/p/2ueqo
Äthiopien Addis Abeba Afrikanische Union Gipfel
Hoto: picture-alliance/AA/M. W. Hailu

Taken wannan taron da na rattaba hannu a tsakanin shugabannin shi ne bude kofofi na cinikayya tare da zama tsintsiya daya madaurinki daya a nahiyarmu ta Afirka. Bincike dai ya tabbatar da cewa wannan yunkuri zai kasance mafi girma a wannan duniya musamman ta fannin cinikayya tun bayan kafa kungiyar cinikayya ta duniya .
Bugu da kari kusan shekaru 40 kenan kasashen ke da burin tabbatar da wannan aniya. Sai yanzu inda kasar Ruwanda bisa jagorancin Shugaba Paul Kagame a matsayinsa na sabon shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika.

To sai a Najeriya kasar da ake mata lakabi da uwa ga sauran kasashen nahiyar Afirka, masana ilmin cinikayya da masu masana'antu da kungiyar kwadago ta kasa sun ja kunnen shugabannin Najeria da su yi hattara bisa cewa hakan ka iya cushe kasuwar cikin gida da kayan kasashen waje musamman daga Kasar Sin. Kan haka ne shugabannin su ka yi hannunka mai sanda ga Shugaba Buhari cewa za a iya haifar da rashin aikin yi baya ga dakushe fannin tattalin arzikin kasa idan har Najeriya ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniya da ke tsakanin kasashen na Afrika.

Muhammadu Buhari
Hoto: DW/I. U. Jaalo

A bisa wannan hujja a yanzu haka Shugaba Buhari na Najeriya ya amince da janye sanya hannu ga wannan doka har sai masana sun sake tattaunawa a kan haka .
Dr Kayode Idowu mai mallakar wata masanaanta ce ta Roba a Kudu maso yammacin Najeriya ya ce kamata ya yi shugaban ya halarci wannan taro:

"Halartar wannan taro ga shugaban Najeriya wata alama ce ta sanya karfin zuciya ta fannin zama uwa ga sauran kasashen Afirka, amma rashin zuwansa ya haifar da komabaya ga kimar Najeriya a idanun duniya wanda zuwansa kadai zai nuna aladunmu na gargajiya da ake aibata sunan Najeriya a kowane lokaci a baya "

Ruanda vor den Wahlen 2017
Hoto: Imago/Zumapress/M. Brochstein

Shi kuwa Mr Mathew Okechuku dan kasuwa ne na kasa da kasa ya ce ko kadan Najeriya matakin da ta dauka bai dace ba:

"Gwamnati ta ce ta janye zuwanta birnin Kigali sabili da koke-koke da wasu ke yi a cikin kasa amma kuma za a iya samun matsala a nan gaba saboda matsayin Najeriya a Afirka ya fi karfin ta ja da baya a duk wani batu na hada-hadar cinikayya a tsakaninsu"

Babu shakka 'yan Najeriya na kuka idan har sun tsinkayi 'yan wasu kasashe makwabta a cikin kasar ga misali an yi Ghana must Go da sauran kasashe kuma mamayewar 'yan wasu kasar da sunan kasuwanci a cikin gida Najeriya matsala ce. 
A Najeriya dai yawancin 'yan kasar sun dagawa Shugaba Buhari tuta bisa yadda yake gyaran kasar.