1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na shirin sake gina arewa maso gabas

Abdul-raheem Hassan
July 25, 2017

Gwamnati ta kaddamar da sabon shirin sake gina yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa, ana sa ran shirin na "Bama initiative" zai ci naira miliyan Dubu 16.

https://p.dw.com/p/2h7nN
Reparaturen an zerstörtem Gerichtsgebäude in Konduga Nigeria
Hoto: Reuters/Stringer

Shirin na Bama initiative dai na zaman irinsa na farko da gwamnatin Najeriya ta kirkiro, da nufin sake farfado da ababen more rayuwar al'ummar arewa maso gabashin kasar da ya sha fama da rikicin Boko Harama. Kama daga makarantu ya zuwa asibitoci da gidajen kwana da massalatai da coci, ana sa ran gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno, za su dauki dabarar sake gini a garururwan da ta'annatin kungiyar Boko Haram ya yi kamari. Kuma ya zuwa yanzu dai an tsara fara shirin daga garuruwan na Bama da Banki da Gulumba Gara da dai sauran garururwa.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria
Gwamnan jihar Borno, Kashim ShettimaHoto: DW

 

 

A yanzu dai gwamnatin kasar ta ware tsabar kudi har naira miliyan Dubu 16,  domin fara shirin da zai kunshi ginin gidaje 3,000 da manya da kananan makarantu 18 sannan kuma da ofisoshin 'yan sanda 10 a karon farko.

Ya zuwa yanzu dai an tsara gwamnatin za ta ba da guddumowa ta kaso biyu a cikin uku na daukacin kudaden da ake bukata a yayin da jihar Borno za ta samar da kaso daya cikin ukun a wani abun dake zaman hadin gwiwar farko ga kokari na komawar yankin ya zuwa dai dai. To sai dai kuma ko bayan sake farfado da ababen more rayuwar al'umma, a karkashin shirin da ke zaman mai fadi gwamnatin kasar za ta horar da maharba 1,500 sannan kuma da wata runduna ta musamman a cikin yankin ko bayan rundunar samar da tsaro ta farin kaya duk dai da nufin kwantar da hankulan al'ummar da ke shirin komawa ya zuwa yankin.

Nigerien Maiduguri Autobombe Doppelanschlag März 2014
Hoto: Getty Images/AFP

Ko bayan nan dai akwai likitoci 20 da jami'an jin kai na lafiya 100 da za su yi aikin samar da bukatu a karkashin shirin da gwamnatin. Abun jira a gani dai na zaman tasirin shirin da ke da burin sake tsugunar da 'yan gudun hijira kusan miliyan biyu da rabi da ke gudun hijira a sassa daban daban ciki da ma wajen kasar.