1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabuwar barazanar zazzabin Lassa

Salissou Boukari
January 24, 2018

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da barkewar cutar zazzabin Lassa a sassa daban-daban na kasar, wanda hakan ke nuni da ci-gaban annobar zazzabin mai zafi.

https://p.dw.com/p/2rT1b
Nigeria | Krankenhaus in Abuja
Babban asibitin Tarayya na Abuja a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Akalla mutane 61 ne dai suka kamu cikin tsawon makonnin biyu a wasu jihohin kasar guda uku na Ebonyi da Ondo da Kogi dama Nasarawa  da ke tsakiyar Tarrayar Najeriyar. Cutar da ke kisa cikin sauki, da kuma ake ta'allakawa da beraye  ta yi nasarar hallaka mutane shida da suka hada da mai'aikatan kiwon Lafiya a cewar ministan lafiya na Tarayyar Najeriya Farfesa Isaac Adewale inda yake cewa:

"Tun daga wannan wata na Janairu mun samu akalla bullar cutar a jikin mutane 61 a daukacin kasar. Ciki  akwai asarar rayuka guda shida. Biyu a Jihar Ondo daya, a  Ebonyi da kuma daya, a Jihar Kogi. Kuma abun damuwar shine mutuwar ma'aikatan lafiya guda uku, sannan mun bi diddigin abun mun tarar da asarar rayuka guda biyun da kuma kamuwa da cutar guda bakwai da wani mai aikin fida a Ebonyi lamari ne da ya saba ka'idar aikin likita, domin idan kana aikin fida ko kana daukar jini to dole ka sanya safar hannu kuma dole ka sanya riga ta kariya domin kar ka fuskanci barazana, wannan ne a tunanina bai faru ba.

Ärzte kämpfen weiter um das Leben des Lassa-Patienten
Likitoci masu kula da masu cutar zazzabin LassaHoto: picture-alliance/dpa

Tun daga shekara ta 1969  ne Tarrayar Najeriyar ke fama da annobar zazzabin na Lassa mai zafi da kuma kan kai ga zubar da jini da asarar rayuka a lokaci kankane. Kuma a kusan duk shekara Tarrayar Najeriyar na asarar rayuka da daman gaske sakamakon cutar da ta dauko asali daga garin Lassa da ke cikin Jihar Borno. Kuma babbar matsalar a fadar Minista Adewale na da ruwa da tsaki da kuskure na fahimta a tsakanin cutar ta Lassa da ta cizon sauro da ke zaman ruwan dare a cikin kasar.

"Ana iya shawo kan Lassa Fever tana iya zama tarihi. Amma abun damuwa shine irin kulawar da take samu. Kamar 'yan Najeriya na daukar zazzabin Lassa kamar zazzabin cizon sauro. Kuma kuskure ne. ya kamata mu rika tunanin Lassa ya kamata mu rika aiki kamar Lassa. Duk wani likitan da ke bada magani na zazzabi ya kamata ya fara tunanin Lassa ko da kuwa ba ita ce ba. Saboda in ka dauka Lassa ce ka sha magani cikin sauri, to kana iya maganinta, ammain ka dauka zazzabin cizon saure ne a cikin satin farko sannan kuma ka sauya shawara zuwa zazzabin Typhoid a cikin mako na biyu, to lokacin da jini ya fara kwarara ga majinyaci ko majinyaciya to kuma an makara”.

Ebola / Virologe / BSL
Likita mai binciken cutar zazzabin LassaHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai kuma a dai dai lokacin da Najeriyar ke neman mafita ta zazzabin Lassan mai zafi, mahukuntan kasar na kuma nazarin wani sabon zazzabi na adawa daga tsohon shugaban kasar Chief Olusegun Obasanjo. To sai dai kuma bayan share tsawon wuni guda suna ganawa, gwamnatin ta ce kalaman na Obasanjo na zaman alamun nasara ga gwamnatin sannan kuma ra'ayinsa ne da bashi da niyyar bata mata rai a fadar mallam garba Shehu da ke zaman kakaki na gwamnatin. Sai dai abun jira a gani na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin mazauna fadar da suka nemi taimako na shugaban wajen darewa kan mulki, da kuma shugaban da ke neman da su koma gida su huta yanzu.