1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shirin samar da takin zamani

February 28, 2017

A kokarinta na kai wa ga tabbatar da dogaro da kai ga abinci, gwamnatin Tarrayar Najeriya ta kaddamar da wani gagarumin shirin samar da takin ga 'yan kasar manoma a farashi mai sauki.

https://p.dw.com/p/2YPE5
Symbolbild Afrika Bewässerung
Manomi a gonarsa ta shinkaraHoto: Getty Images

Kama daga shinkafa ya zuwa ga alkama dama tumaturi dai, sannu a hankali Tarayyar ta Najeriya na kara matsawa ga wadatar da kai da abinci a karkashin wani shirin samar da aiyyuka ga 'yan kasa da ma rage kashe dalar da ke illa ga batu na tattalin arziki. Ko a bana dai akalla ton miliyan biyu da kusan rabi ne dai kasar ta kai ga nomawa na shinkafar, a yayin kuma da ta ke fatan kara yawa na alkamar da ta ke samarwa daga tan dubu dari hudu ya zuwa dubu dari bakwai, kamun karewar daminar da ke tafe.

Kokarin wadata Najeriya da abinci 

Reisanbau in Nigeria
Masu sussukan shinakan da suke nomawaHoto: DW/S. Duckstein

To sai dai kuma na kan gaba a cikin alamun hasken, na zaman wani sabon shirin wadatar da manoma da taki na zamani da gwamnatin kasar ta kaddamar a wannan mako. Shirin kuma da ke da burin samar da akalla ton milliyan daya na takin zamani cikin kasar, kafin karshen bana. Tun a makon farko dai shirin ya kai ga samar da ton dubu hudu na takin ga manoma a farashin  Naira 5,500 ga ko wane buhu. Adadin kuma da ke zaman kusan kaso 60 cikin 100 na farashin kasuwa da ke a tsakanin 8,500 zuwa 9,000 a halin yanzu.

Babban burin Gwamnatin Najeriya kan yawaitar abinci

Nigeria - Landwirtschaft bei Katsina
Masu noma da shanu a Katsina NajeriyaHoto: AP

Gwamnatin kasar dai na fatan takin zai iya kai ga wadatar da kasar da abinci a cikin farashi mai rahusa, ga 'yan kasar da ke kukan ta yi baki  ta lalace ga batun tsada na abinci. Kuma ko bayan nan dai kasar na fatan hakan zai kara dora ta a mizane mai kyau ga kokarin fitar da abincin akalla zuwa ga makwabta dama sauran kasashen duniya a nan gaba. A baya dai Tarrayar Najeriyar ta share tsawon lokaci tana fuskantar matsala ta karancin takin da ke zaman karfen kafa a kokari na wadatar da kasar da isheshen abinci.