1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi

November 25, 2010

Bayan yajin aikin gargaɗi da ma'aikata a Najeriya suka yi, ƙasar za ta miƙa shirin dokar ninka albashi sau biyu

https://p.dw.com/p/QIc4
Shugaba Goodluck JonathanHoto: AP

Majalisar ba da shawara a Tarayyar Najeriya ta ce shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai miƙa shirin dokar da ya tanadar da a ninka mafi ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar, sau biyu zuwa majalisar dokokin ƙasar. Ana sa ran wannan zai biya buƙatun ma'aikata, bayan yajin aikin da suka gudanar a ƙasar a wannan watan.

Ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar dai sun yi yajin aikin gargaɗi makonni biyu da suka wuce domin neman ƙari na mafi ƙarancin albashi daga Naira dubu bakwai da ɗari biyar zuwa dubu 18 wanda yaya daidai da dala 120 na ƙasar Amirka. Majalisar ba da shawarar wadda ta haɗa da shugaba Goodluck Jonathan, da tsoffin shugabanin ƙasar da gwamnoni, da shugaban babban Bankin Najeriya, da wasu manyan ministoci ta ce ta amince da cewa Jonathan ya aika da shirin dokar ne bayan da ta tattauna dalla dalla na wani tsawon lokaci.

A ɗaya ɓangaren kuma shigowa da mugayen makamai ta haramtattun hanyoyi na cigaba da firgita al'ummar ƙasar musamman ma yanzu, da lokacin zaɓe ke gabatowa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Mohammad Nasiru Awal