1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta amince janye dakarunta daga Bakassi

June 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuuJ

Gwamnatin Najeriya ta amince ta janye dakarunta daga yankin Bakassi mai arzikin man fetur cikin kawanki 60,cikin wata yarjejemniya tsakaninta da kamaru.

An samu cimma wannan yarjejeniya ce,wajen wani taron sulhu da majalisar dinkin duniya ta shirya tsakanin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da takwaransa na Kamaru Pauk Biya wajen birnin New York.

Rikicin kan iyaka ya haddasa tashe tashen hankula tsakanin makwabtan biyu a farkon shekarun 1990.

Sakataren Majalisar dinkin duniya Kofi Annan yace,bangarorin biyu sun bashi iznin kara kwanaki 30 domin kammala janye dakarun na Najeriya.