1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta biya 'yan wasa bashinsu

Yusuf Bala Nayaya
December 16, 2016

A ranar Laraba ne dai 'yan wasan Falcons suka gabatar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar inda suka sha alwashi na rike kofi da ma lambobin girma da suka samu.

https://p.dw.com/p/2UQdt
Flash-Galerie Frauenfußball WM Nationalmannschaft Nigeria
Hoto: picture alliance/Sven Simon

Gwamnatin Najeriya ta saki kudi sama da Dala miliyan daya dan biyan alawus-alawus na tawagar 'yan wasan kwallon kafa a kasar. Ofishin akanta janar na gwamnatin Najeriya ya ce kudin da aka fitar Dala miliyan daya da dubu dari biyu ne wadanda za a bayar ga 'yan wasan Super Falcons saboda rawar da suka taka a gasar wasan kwallon kafa ta mata ta Afirka da aka buga a Kamaru, da ma kudin wasanni na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da suka buga wasan share fagen zuwa gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2018 kamar yadda jami'ai suka bayyana.

A ranar Laraba ce dai 'yan wasan Falcons suka gabatar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar inda suka sha alwashi na rike kofi da ma lambobin girma da suka samu har sai gwamnatin kasar ta biya su alawus-alawus nasu.