1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta fitar da sunayen 'yan Chibok da suka tsira

May 8, 2017

Fadar shugaban kasar Najeriya, ta fitar da jerin sunayen 'yan matan makarantar Chibok 82 da kungiyar Boko Haram ta sako a karshen mako. 

https://p.dw.com/p/2cbtk
Nigeria freigelassene Chibok Mädchen in Abuja
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Gbemiga

Mahukuntan Najeriyar sun fidda sunayen ne bayan ganawar da shugaba Buhari ya yi da su da yammacin jiya Lahadi, inda daga bisani ya mike birnin Landan na Birtaniya don sake bibiyar lafiyarsa.

Iyayen yaran na Chibok dai na cike da zumudin ganin 'ya'yan na su da suka dauki shekaru uku cur a dajin Sambisa, babbar tunga ta mayakan na tarzoma. 'Yan Najeriya masu yawa na ta zagaya runfunan jaridun kasar don ganin sunayen 'yan matan da suka tsira.

Tuni ma dai wasu daga cikin iyayen 'yan matan suka kasance a Abuja fadar gwamnatin kasar a kokarin ganin 'ya'yan na su. Jami'an na Najeriyar dai sun ce an yi musayar 'yan matan da kwamandoji biyar na Boko Haram, da dama ke tsare.