1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta soke kwangilar kanfanin Siemens

December 6, 2007
https://p.dw.com/p/CXjb

Najeriya ta soke kwangilarta ta ƙarshe da kanfanin nan na Jamus Siemens ta kuma dakatar da dukkan hulɗa da kanfanin har sai bayan an kammala bincike kan zargin da ke cewa kanfanin ya bada cin hanci na euro miliyan 10 ga wasu jamian Najeriya.Wata kotu a nan Jamus ta ci tarar kanfanin fiye da euro miliyan 200 a watan Oktoba bisa laifin bada cin hanci ga jamian ƙasashen Najeriya da Rasha da kuma Libya.A watan da ya gabata jaridar Wall Street ta bada rahoton cewa tsoffin ministoci da manyan jamian Najeriya 5 suke da hannu cikin wannan cin hanci.Shugaba Umar Yar Aduwa dai ya ya ƙuduri aniyar yaƙi da cin hanci da rashawa tun lokacinda ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayu haka kuma ya baiwa hukumomin tsaro umurnin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace. Gwamnatin ta Najeriya tace har sai binciken ya wanke Siemens kafin ta koma hulda da ita,