1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsare Diezani Alison Madueke a birnin London

Kamaluddeen SaniOctober 5, 2015

Mahukuntan tarayyar Najeriya sun tabbatar da tsare tsohuwar ministar harkokin man fetur Diezani Alison Madueke a birnin London a bisa zargin cin hanci da mallakar kudaden haram.

https://p.dw.com/p/1Giuj
Österreich Wien 166. OPEC Konferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Pfarrhofer

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Najeriya Garba Shehu shi ne ya tabbatar da hakan a inda ya kara da cewar Najeriya na sane da tsarewar da aka yiwa tsohuwar ministar a birnin London.

Yace an sanar da gwamnatin Najeriya kana kuma jami'an ma'aikatar tsaro tuni suka fara aiki kafada da kafada da jami'an kasar Britaniya kan wannan al'amarin.

Diezani yar shekaru 59 ta kasance ministar harkokin man fetur ne a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tun daga shekara ta 2010 zuwa 2015 a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya doke shi a babban zaben kasar da aka gudanar dake tatare da tarihi a shekara ta 2015.

A yau ne dai ministar take sake komawa ofishin binciken manyan laifuka dake a london don cigada da fuskantar tuhume-tuhuman da ake mata.