1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Takaddama kan sanya hijabi na wata lauya

Mansur Bala Bello | Gazali Abdou Tasawa
December 19, 2017

A Najeriya cece-kuce ake cigaba da yi dangane da matakin da makarantar horas da lauyoyi ta kasa ta dauka na haramta wa Firdausi Amara Abdulsalam damar kammala karatunta na lauya a bisa dalilin saka hijabi.

https://p.dw.com/p/2pfh4
Nigeria Gerichtshof in Abuja
Hoto: DW/U. Musa

 

Firdausi Amara Abdulsalam ta kasance cikin tsaka mai wuya bisa dakatar da ita da aka yi daga kamala karatunta na lauya bisa amfani da hijabi. Hakan dai ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya daga bangaren Musulmi a Najeriya inda har ta kai kungiyar Musulmin kasar ta shirya wani taro na fadakar da hukumar makarantar da Firdausin ke karatu.

Nigeria Flüchtlingslager Maiduguri - Fatima Ali entkam Boko Haram
Mutane da kungiyoyi da dama na ta fafutukar ganin an bar lauyoyi mata su rika sanya hijabi a loakcin da ake rantsar da suHoto: picture-alliance/dpa/K. Palitza

A taron gangamin da ta gudanar a Legas, guda daga cikin kungiyoyin Musulmin kasar ta yi kira ga hukumar makarantar da ta janye matakinta na korar dalibar mai karantun lauya, matakin da kungiyar ta ce ya ci zarafin Firdausi tare da tauye mata hakki na yin addininta. Bayan kawo hujjoji masu karfi daga cikin littafi mai tsarki na Musulmai da ke nuni da cewa addinin Islama ya tabbatar da cewa sanya hijibi ga mace tamkar addini ne.

Shugabannin Musulunci sun bayyana matsayinsu kan hukuncin da makarantar horar da lauyoyin ta Najeriya ta dauka da cewa ya saba wa dokar tsarin mulkin Najeriyar. A kan haka ne ma shugaban gamgamin Musulmin Parfesa Ishaq Akintola ya yi kira ga illahirin Muslmin Najeriya da su farka daga barci domin daukar matakan da shari'a ta tanada domin fitarwa da Firdausi hakkinta a cikin wannan lamari tun kafin ya fada hannun bata gari.

Nigeria Kano Mädchen Nijab
Dalibai mata a Najeriya musamman a arewaci kan kasance cikin hijabi a makarantu da sauran wuraren haduwar jama'aHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shugaban kungiyar Musulmi kabilar Igbo Malam Abdulkabir Muhamadu Ojogbo ya ce kare Musulunci ya zama wajibi ga duk wanda ya amsa sunan Musulmi a doron kasa kuma matukar mace Musulma ce dole ne ta sanya Hijabi domin haka shari'a ta tanada ga Musulmin duniya. Yanzu haka dai lauyoyi da dama ne maza da mata a tarayyar ta Najeriya suka sha alwashin kare a gaban shari'a Firdausin wacce wasu ke kallonta a matsayin wata gwarzuwar mace a kasar.